Addu’ar tafiya

1

(207) Allah ne Mafi girma. Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma. Tsarki ya tabbata ga (Ubangiji) Wanda ya hore mana wannan (abin hawa); ba mu kasance masu ikon sarrafa shi ba. Hakika mu masu komawa ne zuwa ga Ubangijinmu. Ya Allah! Muna rokon Ka nagarta da tsoron Allah a cikin wannan Lafiya ta mu. da kuma aiki wanda Kake yarda da shi. Ya Allah! Ka saukake mana wannan tafiya ta mu kuma ka nade mana nisanta. Ya Allah! Kai ne Ma’abocinmu a cikin wannan tafiya. kuma Halifanmu a cikin iyalanmu. Ya Allah! Ina neman tsari da Kai daga wahalar tafiya da abin gani mai sanya bacin rai. da kuma komawa mummuna ga iyali da dukiya. Idan ya dawo daga tafiyar tasa, Sai ya fadi wannan addu’a kuma ya kara da cewa: Mu masu komowa ne. masu tuba. masu bauta. kuma masu godiya ne ga Ubangijinmu.

Zaker copied