Addu’ar tashi daga majlisi (domin neman yafewa ga abin da ya gudana a cikin majlisin)

1

(196) A’isha, Allah ya yarda da ita, ta ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taba zama a wani majlisi ba, ko ya karanta Alkur’ani, ko ya yi wata sallah face ya cika da wadannan kalmomi: Tsarki ya tabbata gare Ka. ya Allah, da yabo gare Ka. Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai; ina neman gafararka. kuma ina tuba zuwa gare Ka. Sai A'isha ta ce: Ya Manzon Allah. Na lura cewa ba ka taba zama a wani majlisi ba, ko ka yi karatun .Alkur'ani, ko ka yi sallah face ka fadi wadannan kalmomi. Sai ya ce: kwarai, Duk wanda ya fadi wani alheri sai wadannan kalmomi su zama kamar hatimi ne ga alherin da ya aikata wanda kuma ya fadi sharri, sai su zama kaffara ne gare shi.

Zaker copied