(195) Ibn Umar ya ce: an kasance ana kirgawa ga Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a majlisi guda kafin ya tashi, yana cewa sau dari: Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, Ka yi tuba a gare ni. Lallai Kai ne Mai yawan karbar tuba, Mai yawan gafara.