(191) Idan dayanku ya auri mace, ko ya sayi bawa mai hidima, to ya ce: Ya Allah! Ina rokon Ka alherinta da alherin da Ka dabi'antar da ita akansa; kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin da Ka dabi'antar da ita a kansa. Idan kuma ya Sayi rakumi, to ya kama tozon Rakumin ya fadi kwatankwacin wannan (addu ’ar).