(188) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: idan dayanku ya yi atishawa to ya ce: Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. Dan uwansa kuma ko wanda yake zaune tare da shi ya ce masa: Allah ya ji kanka. Idan ya gaya masa haka, shi kuma ya ce masa: Allah Ya shirye ku, Ya kyautata halinku.