Addu’ar cin abinci

1

(178) ldan mutum zai ci abinci sai ya ce: Da Sunan Allah. Idan ya manta to sai ya ce (yayin da ya tuna): Da sunan Allah a farkonsa da karshensa.

2

(179) Wanda Allah ya ciyar da shi abinci, to ya ce: ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinsa. kuma Ka ciyar da mu Wanda ya fi shi alheri. Wanda kuma Allah ya shayar da shi madara, to ya ce: Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinta, kuma Ka Kara mana ita (madarar).

Zaker copied