Daga cikin addu’o’in rokon ruwa

1

(169) Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama mai yaye tsanani, mai dadi, mai ni’ima. mai amfani ba mai cutarwa ba. da gaugawa ba da jinkiri ba.

2

(170) Ya Allah! Ka ya mana agaji (da ruwan sama). Ya Allah! Ka yi mana agaji. Ya Allah! Ka yi mana agaji.

3

(171) Ya Allah! Ka shayar da bayinka. da dabbobinka; kuma Ka yada Rahamarka, Ka rayar da kekasasshiyar kasarka.

Zaker copied