(165) Aminci ya tabbata a gare ku, ya ku ma’abota wadannan gidaje daga muminai da musulmi, kuma mu in Allah ya so masu riskuwa ne da ku. Kuma Allah ya ji Kan wadanda suka gabata daga cikinmu da wadanda suka yi saura. Ina rokon Allah aminci daga bala’i gare mu da gare ku.