Addu’a bayan an binne mamaci

1

(164) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan aka gama binne mamaci. sai ya ce: ku nema wa dan uwanku gafara, kuma ku roka masa tabbatuwa, domin yanzu ne ake yi masa tambayar kabari . Ya Allah! Ka gafarta masa. Ya Allah! Ka ba shi tabbata.

Zaker copied