Addu’a ga mamaci yaro yayin Sallar jana’iza a gare shi

1

(160) Ya Allah! Ka tsirar da shi daga azabar kabari. Idan kuma ya karanta wannan addu ’ar to yana da kyau; an same ta daga cikin littattafan malamai. Ya Allah! Ka sanya shi lada abin gabatarwa, abin ajiyewa ga iyayensa kuma mai ceto wanda ake karbar cetonsa. Ya Allah! Ka nauyaya ma'aunan ayyukansu da shi. Ka girmama ladaddakinsu da shi, kuma Ka Iiskar da shi da salihan muminai, Ka sanya shi cikin renon Annabi Ibrahim. Ka tserar da shi da rahamarka daga azabar wuta, Ka musanya masa gida da ya fi gidansa alheni, da iyali da suka fi iyalinsa alheri. Ya Allah! Ka gafarta wa wadanda suka riga mu (gidan gaskiya) da ’ya’yanmu da suka riga mu (gidan gaskiya) da wadanda suka gabace mu a cikin imani.

2

(161) Hasan al-Basri ya kasance yana karanta Fatiha a wajen sallar gawa ga yaron do ya mutu sannan ya ce: Ya Allah! Ka sanya shi magabaci. da marigayi, da lada gare mu.

Zaker copied