Addu’ar da ake yi ga mamaci a cikin sallar jana’iza

1

(156) Ya Allah! Ka yi masa gafara, Ka ji kansa, Ka amintar da shi daga bala’i. Ka yi masa rangwame. kuma Ka girmama liyafarsa, Ka yalwata mashigarsa (kabarinsa), kuma Ka wanke shi da ruwa da kankara da ruwan raba Ka tsafiace shi daga laifuffuka kamar yadda Kake tsafiace farar tufa daga dauda, kuma Ka musanya masa gidan da ya fi gidansa alheri, da mutanen gida da suka fi mutanen gidansa alheri, da mata da ta fi matarsa alheri, kuma Ka shigar da shi aljanna, ka tsirar da shi daga azabar kabari da azabar wuta.

2

(157) Ya Allah! Ka gafarta wa rayayyunmu da matattunmu da wadanda suke halarce tare damu da wadanda ba sa nan da yaranmu da manyanmu, da mazajenmu da matayenmu. Ya Allah! Wanda Ka rayar da shi daga cikinmu, to Ka rayar da shi a cikin musulunci. wanda kuma Ka dauki ransa to Ka dauki ransa a kan imani. Ya Allah! Kada Ka haramta mana ladan (hakurin rashinsa), kada kuma ka batar da mu bayansa.

3

(158) Ya Allah! Hakika wane dan wane yana cikin alkawarinka (na kiyayewa) da amanarka; don haka Ka tserar da shi daga fitinar kabari da azabar wuta. Kai ne Ma’abucin cika alkawari da gaskiya; Ka gafarta masa, Ka ji kansa. Hakika Kai. Kai nc Mai yawan gafara, Mai yawan jin kai.

4

(159) Ya Allah! Bawanka kuma dan baiwarka ya bukatu ga rahamarka, kuma Kai Mawadaci ne ga barin azabarsa. Idan mai kyautata aiki ne. Ka yi Kari a cikin kyawawan ayyukansa, idan kuma mai mummuman aiki ne. Ka yafe masa

Zaker copied