Addu’ar mara lafiya da ya yanke Kauna daga rayuwa

1

(150) Ya Allah! Ka gafarta mini, Ka ji Kai na, kuma Ka riskar da ru da abokin zama mafi daukaka.

2

(151) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yayin da ajali ya zo masa, sai ya rinka sanya hannayensa a cikin ruwa yana shafa fuskarsa da su yana cewa: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; hakika mutuwa tana da magagi mai dimautarwa.

3

(152) Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; Allah ne Mafi girma. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. mulki da yabo nasa ne. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma babu dabara babu karfi sai da Allah.

Zaker copied