(149) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Idan mutum ya ziyarci dan uwansa musulmi (da ba shi da lafiya) to yana tafiya ne cikin lambunan aljanna yana tsinkar ’ya 'yan itaciyarsu, idan ya zauna sai rahama ta Lullu be shi. Idan da safe ne mala’iku dubu saba'in za su yi ta yi masa salati har ya shiga maraice. Idan kuma da maraice ne mala’iku dubu saba'in za su yi ta yi masa salati yar ya wayi gari.