(147) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya ziyarci mara lafiya sai ya ce masa:
( 148 ) Ina rokon Allah Mai girma, Ubangijin Al’arshi mai girma. ya warkar da kai. (sau bakwai) Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Babu wani bawa musulmi da zai ziyarci mam lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya fadi? wannan {addu'a) sau bakwai face ya sami lafiya