(144) Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Mummini kakkarfa ya fi alheri kuma ya fi soyuwa ga Allah daga mumini mai rauni, a tare da kowanne daga cikinsu kuma akwai alheri. Ka yi kwadayin abin da zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah; kada ka gajiya. Idan wani abu ya same ka, kada ka ce: da na aikata kaza da kaza, da kaza ya kasance, sai dai ka ce: kaddarar Allah ce. kuma abin da Allah ya so, shi yake aikatawa; domin da-na-sani tana bu de kofar aikin Shaidan.