Addu’ar wanda ya ji tsoron zaluncin wani mai iko

1

(129) Ya Allah! Ubangijin sammai bakwai, kuma Ubangijin Al’arshi mai girma, Ka kasance Mai tsari gare ni daga wane dan wane, da dukkan rundunarsa daga cikin halittunka kar wani daga cikinsu ya yi gaggawar azaba a gare ni, ko ya ketare haddi. Kariyarka ta buwaya, kuma Yabonka ya girma, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Kai.

2

(130) Allah Shi nc Mafi girma. Allah Shi ne Mafi buwaya daga dukkanin halittarsa. Allah Shi ne Mafi buwaya daga abin da nake jin tsoronsa kuma nakc shayinsa. Ina neman tsarin Allah, Wanda babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Mai rike sammai daga su ruguzo a kan Rasa sai da Izininsa. daga sharrin bawanka wane (ya ambaci sunansa), da rundunarsa da mabiyansa, da kungiyoyinsa na aljanu da mutane. Ya Allah! Ka zamo Mai tsani gare ni daga sharrinsu. Yabonka ya girma, kuma Kariyarka ta buwaya kuma alherin Sunanka ya yawaita, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba Kai bi. (San uku)

Zaker copied