Addu’ar tafiyar da Euncin zuciya

1

(122) Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Mai girma (wanda babu abin da yake girmama a gare Shi). Mai hakuri (Maj jinkirin azaba tare da cikakken ikon aiwatar da ita). Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Ubangijin Al'arshi, Mai girma. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Ubangijin sammai. Ubangijin kasa. Ubangijin AI’arshi. Mai yawan baiwa.

2

(123) Ya Allah! Rahamarka nake kauna, don haka Kar Ka kyale ni da kaina ko da kiftawar ido ne, kuma Ka kyautata mini sha’anina dukkansa; babu abin bautawa da gaskiya sai Kai.

3

(124) Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Tsarki ya tabbata gare Ka. lalle ni na kasance daga cikin azzalumai.

4

(125) Allah! Allah ne Ubangijina, ba na yin tarayya da Shi da wani abu a cikin bauta.

Zaker copied