(120) Ya Allah! Ni bawanka ne, kuma dan bawanka, kuma dan baiwarka. Makwarkwadata a Hannunka take, hukuncinka zanacce ne a kai na, kuma Kaddararka gare ni mai adalci ce, Ina rokon Ka da kowane Suna naka. Wanda Ka ambaci Kanka da Shi, ko Ka saukar da Shi a cikin Littafinka, ko Ka sanar da Shi ga wani daga cikin halittarka ko Ka kebance Kanka da sanjnsa a cikin Ilmin fake da ke wurin Ka. da Ka sanya Alkur'ani ya zama kaka ga zuciyata. da haske ga kirjina da kwaranyewa ga bakin cikina. da kuma mai tafiyar da damuwata.
(121) Ya Allah! Ina neman tsarinKa daga damuwa, da bakin ciki, da gajiyawa, da lalaci, da rowa, da ragwantaka. da nauyin bashi, da rinjayen mazaje.