(116) Ya Allah! Ka shirye ni cikin wadanda Ka shiryar. Ka amintar da ni daga mummuna cikin wadanda Ka yi wa aminci daga mummuna, Ka jibinci lamari na cikin wadanda Ka jibinci lamarin su, Ka albarkance ni cikin abin da Ka ba (ni), Ka kiyashe ni sharrin abin da Ka Kaddara. domin Kai ne Kake hukunci. babu wanda yake hukunci a Kanka. Tabbas wanda Ka jibince shi ba zai wulakanta ba wanda kuma Ka Ki shi ba zai daukaka ba. Alherinka ya yawaita, ya Ubangijinmu! Kuma Ka Daukaka.
(117) Ya Allah! Ina neman tsari da Yardarka daga Fushinka. da kuma Rangwamanka daga Ukubarka. kuma ina neman tsari da Kai daga gare Ka. Ban isa in tuke ga yabo mai cancanta gare Ka ba; Kai dai kamar yadda Ka yabi Kanka ne.