Addu’a yayin da za a yi barci

1

(99) Idan mutum ya zo kwanciyar barci sai ya hada tafin hannayensa biyu. ya karanta wad annan surori na Alkur'ani, yana yin tofi cikin hannayen nasa: Sannan ya shafa su iya inda zai iya na jikinsa; yana farawa da kansa, da fuskarsa da kuma gaban jikinsa. Ya yi haka har sau uku.

2

(100) Ya karanta Ayatul Kursiyyu. har zuwa Karshenta. Wanda ya karanta ta yayin da ya zo kwanciya to ba zai gushe ba yana da wani mai tsaro a gare Shi daga Allah, kuma Shaidan ba zai kusato shi ba har ya wayi gari.

3

(101) Manzo ya yi imani da abin da aka saukar gare shi daga Ubangijinsa. haka ma muminai; kowanne ya yi imani da Allah. da mala'ikunsa da littattafansa. da manzanninsa, (suna cewa:) ba ma rarrabewa tsakanin daya daga cikin manzanninsa. Kuma suka ce: mun ji (abin da Ka umarce mu da shi,ji na karba) kuma mun bi. Gafararka muke roko ya Ubangijimnu, kuma gare Ka makoma take, Allah ba ya dora wa rai (wani abu) sai abin daya ke da ikon aikata shi; abin da ya aikata (na alheri) yana gare shi, kuma abin da ya aikata (na sharri) yana kansa. (Ku ce:) Ya Ubangijinmu! Kada Ka riKe mu idan muka manta ko muka yi kuskure. Ya Ubangijinmu! Kada Ka dora abu mai nauyi a kan kamar yadda Ka dora shi a kan wadanda suke gabaninmu Ya Ubangijinmu! Kada Ka dora mana abin da za mu iya shi ba. Ka yi afuwa a gare mu. Ka yi mana gafara Ka ji Kan mu. Kai ne Majibincin al’amuranmu. sai Ka taimake mu a kan mutane kafirai .

4

(102) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya Ce: Idan dayanku ya tashi daga shimfi darsa sannan ya dawo ya kwanta, to ya karkade ta da gefen gvautonsa sau uku, sannan ya yi bisimillah, domin bai San abin da ya maye gurbinsa ba bayan ya tashi. Idan ya kwanta Sai ya ce: Da Sunanka ya Ubangijina na kwanta, kuma da Izininka ne nake tashi. In Ka rike raina (da mutuwa), to Ka ji kanta. in Ka sake ta kuwa, Ka kiyaye ta da abin da Kake kiyaye bayinka salihai da shi.

5

(103) Ya Allah! Kai ne Ka halicci raina, kuma Kai ne Kake karben sa. Gare Ka Kadai mutuwarsa da rayuwarsa sukc. In Ka rayar da shi, to Ka kiyaye shi; in Ka dauke shi, to Ka gafarta masa. Ya Allah! lna rokonka aminci daga dukkan mummuna.

6

(104) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya zo kwanciya sai ya sa hannunsa na dama karkashin kuncinsa, sannan ya ca: Ya Allah! Ka kiyashe ni azabarka a ranar da Kake tayar da bayinka (bayan mutuwa). (Sau uku)

7

(105) Da Sunanka ya Allah nake mutuwa kuma nake rayuwa.

8

(107) Ya Allah! Ya Ubangijin sammai bakwai. Ubangijin Al'arshi mai girma, Ubangjjinmu kuma Ubangijin komai. Mai tsaga Kwayar tsiri da kwallon dabino, Mai saukar da Attaura da Injila, da Alfurkani! Ina neman tsarinka daga sharrin komai wanda Kai ne Mai rike da makwarkwadarsa. Ya Allah! Kai ne Na farko, babu wani abu kafinka, Kai Na karshe, babu wani abu bayanka, Kai ne Bayyananne, babu wani abu da yake sama da Kai, Kai ne Boyayye, babu wani abu da ya ke boyuwa gare Ka. Ka biya mana basussuka. kuma Ka wadatar da mu daga talauci.

9

(106) Tsarki ya tabbata ga Allah. (Sau talatin da uku) Yabo ya tabbata ga Allah. (Sau talatin da uku) Allah ne Mafi girma. (Sau talatin da hudu).

10

(108) Yabo ya tabbata ga Allah, Wanda Ya ciyar da mu, Ya shayar da mu. Ya isar mana. Ya ba mu makwanci, Da yawa wanda ba shi da ma’ishi. wala mai ba shi makwanci.

11

(109) Ya Allah! Masanin abin da ke fake da na sarari! Mai kagen halittar sammai da kassai! Ubangijin komai. kuma Mamallakinsa! Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Ina neman tsarinka daga sharrin raina, da kuma sharrin Shaidan da shirkarsa, da in tsuwurwurtawa kaina wani abu mummuna. ko in jawo shi ga wani musulmi.

12

(110) Ya karanta suratu As-Sajdah (Alif Lam mim, Tanzilul) da suratul Mulk (Tabaraka).

Zaker copied