(75) Ina neman tsarin Allah daga Shaidan. tsinanne. Allah. babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye. Mai tsayuwa da komai. Gyangadi ba ya kama Shi. wala barci. Abin da ya ke cikin sammai da da abin yake cikin Kasa nasa ne. Babu mai yin ceto a wurinsa sai da izininsa. Yana sane da abin da yake gabansu (wato al’amarin duniya) da abin da yake bayansu (na al’amarin lahira). Ba sa sanin wani abu daga iliminsa, sai abin da Ya so. Kursiyyunsa (wato gadonsa) ya yalwaci sammai da Kasa, kuma kiyaye su (sammai da Kassai) ba ya yi masa nauyi. Shi ne kuma Madaukaki Mai girma.
(76) Ana karanta wadannan surorin (kowacce daga Ciki har zuwa Karshenta) bayan sallar Asuba da bayan sallar Magariba sau uku.
(77) Mun wayi gari, kuma mulki ma ya wayi gari yana mai tabbata ga Allah. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, mulki ya tabbata gare Shi. Kuma yabo ya tabbata gare Shi, kuma Shi Mai iko ne bisa komai. Ya Ubangijina! Ina rokonka alherin da ke cikin wannan rana, da alherin da ke bayanta. Kuma ina neman tsarinka daga sharrin da ke cikin wannan rana da sharrin da ke bayanta. Ya Ubangijina! Ina neman tsari da Kai daga lalaci, da mummunan tsufa. Ya Ubangijina! Ina neman tsari da Kai daga azaba a cikin wuta, da kuma azaba a cikin Kabari. Idan kuma da maraice ne sai ya ce: Mun shiga maraice, kuma mulki ma ya shiga maraice yana mai tabbata ga Allah... Ya Ubangijina! lna rofionka alherin da ke cikin wannan dare da alherin da ke bayansa. Kuma ina neman tsarinka daga sharrin da ke cikin wannan dare da sharrin da ke bayansa
(78) Ya Allah! Da Ikonka ne muka wayi gari, kuma da Ikonka ne muka shiga maraice, kuma da Ikonka ne muke rayuwa. kuma da Ikonka ne muke mutuwa, kuma izuwa gare Ka ne matattara take. Da yamma kuma sai ya ce: Ya Allah! Da Ikonka ne muka shiga maraice. kuma da lkonka ne muka wayi gari, kuma da Ikonka ne muke rayuwa. kuma da Ikonka ne muke mutuwa, kuma izuwa gare Ka ne makoma take.
(79) Ya Allah! Kai ne Ubangijina; babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Ka halicce ni, kuma ni bawanka ne; kuma ina kan alkawarin da na yi maka (na kadaitaka da bauta) da kuma alKawarin da Ka yi mini (na shigar da wanda bai yi shirka da Kai ba gidan aljanna) gwargwadon ikona. Ina neman tsarinka daga sharrin abin da na aikata. Ina tabbatar da ni'imarka gare ni. kuma ina tabbatar da zunubi na; Ka gafarta mini, domin ba wanda yake gafarta zunubai sai Kai. Wanda ya karanta wannan addu'a da maraice yana mai imani da ita, idan ya mutu a cikin daren zai shiga aljannz; hakanan ma idan ya karanta ta da safe.
( 80 ) Ya Allah! Ni na wayi gari ina shaidawa gare Ka. kuma ina shaidawa ga (mala'iku) masu (daukan Al’arshinka. da mala'ikunka da dukkan halittarka cewa Kai, Kai ne Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Kai Kadia, babu abokin tarayya a gare Ka, kuma Muhammadu Bawanka ne kuma Manzonka ne. (sau hudu) Wanda ya karanta kamar yadda aka ce Allah zai yanta shi daga wuta.
(81) Ya Allah! Dukkan abin da ya wayi gari a gare ni na ni’ima, ko ga wani daga cikin halittarka, to daga gare Ka ne. Kai Kadai, babu abokin tarayya a gare Ka; kuma yabo ya tabbata a gare Ka kadai, kuma godiya ta tabbata a gare Ka kadai. Wanda ya fade ta da safe to wannan ya cika godiyar ranarsa, wanda kuma ya fada da yamma ya cika godiyar darensa.
(82) Ya Allah! Ka ba ni lafiya (aminci daga bala’i) a jikina. Ya Allah! Ka ba ni lafiya a jina. Ya Allah! Ka ba ni lafiya a ganina. Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Ya Allah! Ina neman tsarinka daga kafirci da talauci, kuma ina neman tsarinka daga azabar kabari. Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. (Sau uku)
(83) Allah Ya ishe ni, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi. A gare Shi kadai na dogara. Shi ne Ubangijin Al’arshi mai girma. (sau bakwai da safe da maraice). Wanda ya karanta ta kamar yadda aka Ce, Allah zai ishe masa duk abin da ya dame shi na al'amarin duniya da na lahira.
(84) Ya Allah! Ina rokonka afuwa da aminci daga dukkan mummuna a duniya da lahira. Ya Allah! Ina rokonka afuwa da aminci daga dukkan mummuna a addinina, da duniyata. da iyalina, da dukiyata. Ya Allah! Ka yi mini suture, Ka kwantar da hankalina. Ya Allah! Ka kiyaye ni ta gabana, da ta bayana da ta damana, da ta haguna da ta sama da ni, kuma ina neman tsari da Girmanka da a kisfe Kasa da ni.
(85) Ya Allah! Masanin abin da ke fake da na sarari! Mai Kagen halittar sammai da Kassai! Ubangijin komai. kuma Mamallakinsa! Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Ina neman Tsarinka daga sharrin raina, da kuma sharrin Shaidan da shirkarsa. da in tsuwurwurtawa kaina wani abu mummuna, ko in jawo shi ga wani musulmi.
(86) Da Sunan Allah, Wanda da Sunansa wani abu a sarna ko a Kasa ba ya cutarwa. Shi ne Mai ji. Masani. (Sau uku) Wanda ya fada Sau uku da Safe da yamma wani abu ba zai cutar da shi ba.
(87) Na yarda da Allah Ubangiji. da musulunci addini. da Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Annabi. (Sau uku)
(88) Ya (Allah) Rayayye, Mai tsayuwa da komai! Da Rahamarka nake neman agaji. Ka kyautata mini sha'anina dukkaninsa. kada Ka kyale ni da kaina ko da daidai da kiftawar ido ne.
(89) Mun wayi gari, kuma mulki ma ya wayi gari yana mai tabbata ga Allah. Ubangijin talikai. Ya Allah! Ina rokonka alherin wannan rana: Budinta, da nasararta, da haskenta, da albarkata. da shiriyarta, Kuma ina neman tsarinka daga sharrin abin da ke cikinta. da abin da ke bayanta. Da yamma kuma sai ya ce: Mun shiga maraice, kuma mulki ma ya shiga maraice yana mai tabbata ga Allah.
(90) Mun wayi gari a kan Kirar da Allah ya yi mana ta Musulunci, kuma a kan kalmar tauhidi, kuma a kan addinin Annabinmu Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gate shi. kuma a kan addinin Babanmu Ibrahim, mai totar zuwa ga addinin gaskiya. musulmi, bai kasance daga cikin mushrikai ba.
(91) Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da godiya gare Shi. (Sau dari) Wanda ya karanta sau dzri yayin da ya wayi gari da kuma yayin da ya shiga maraice, ranar Kiyama ba wanda zai zo da aikin da ya fi abin da ya zo da shi afalala sai wanda ya karanta kamar yadda ya karanta ko sama da haka.
(92) Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi Kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki nasa ne Shi Kadai. yabo ma nasa ne Shi Kadai, kuma Shi Mai iko ne bisa komai. (Sau goma, ko sau daya idan ya ji kasala)
(93) Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi Kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki nasa ne Shi Kadai, yabo ma nasa ne Shi Kadai. kuma Shi Mai iko ne bisa komai. (Sau dari idan ya wayi gari) Wanda ya fa da sau a rana kamar ya yanta bayi goma ne, kuma za a rubuta masa kyakkyawan aiki dari, a shafe masa mummunan aiki dari kuma ita addu'ar za ta zamo masa tsari daga Shai dan a tsawon wannan rana har ya kai maraice, kuma ba wanda zai yi aikin da ya fi nasa falala sai wanda ya karanta fiye da haka.
(94) Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da yabo gare Shi, iya adadin halittunsa. da gwargwadon yardar Kansa, da iya nauyin Al’arshinsa, da iya (Sau uku da safe)
(95) Ya Allah! Ina rokon Ka ilimi mai amfani, da arziki na halal, da aiki karbabbe. (Da safe)
(96) Ina neman gafarar Allah, kuma ina tuba zuwa Gare shi (Sau dari a rana)
(98) Ya Allah! Ka yi salati da aminci ga Annabinmu Muhammadu. Sau goma.