(74) Jabir ibn Abdullah, Allah ya yarda da shi da mahaifinsa, ya Ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, ya kasance yana koya mana yin istihara (neman zabin Allah) a cikin dukkan al’amura kamar yadda yake koya mana sura daga cikin Alkur’ani, yakan Ce: Idan dayanku ya yi niyyar yin wani al’amari to ya yi sallah raka’a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce: Ya Allah! Ina neman zabinka domin Iliminka, kuma ina neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonka daga Falalarka Mai girma; domin Kai ne Mai iko, ni kuwa ba ni da iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne Masanin abubuwan fake. Ya Allah! Idan Ka san cewa wannan al’amari -sai ya ambaci bukatar tasa - alheri ne gare ne a cikin addinina, da rayuwata, da kuma karshen al’amarina - a wata ruyuayar: da magaggaucin al’amarina da majinkircinsa - Ka Kaddara mini shi. kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkance ni a cikin sa. Kuma idan Ka san wannan al’amari sharri ne gare ni a cikin addinina. da rayuwata, da Karshen al’amarina - a wata ruwayar: da magaggaucin al’amarina da majinkircinsa - Ka kawar da shi daga gare ni, kuma Ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka Kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma Ka sanya In in yarda da shi. Duk wanda ya nemi zabin Mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma ya yi azama a cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba, domin Allah Madaukalin Sarki ya ce: Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka Kuduri aniya. to ka dogara ga Allah .