Zikirin bayan an yi sallama daga sallah .

1

(66) Ina neman gafarar Allah (sau uku) Ya Allah! Kai ne Aminci, kuma daga gare Ka aminci ya ke. Alherinka ya yawaita, ya Ma'abocin girma da alheri.

2

(67) Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Shi kadai. babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki na Sa ne (Shi kadai). kuma yabo na Sa ne (Shi kadai), kuma Shi ne Mai iko a kan komai. Ya Allah! Babu mai hana abin da Ka bayar. kuma babu mai bayar da abin da Ka hana. kuma wadata ba ta tsirar da mai wadata daga gare Ka.

3

(68) Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Shi kadai. babu abokin tarayya a gare Shi. Mulkj na Sa ne (Shi kadai). kuma yabo na Sa ne (Shi kadaj). kuma Shi ne Mai iko a kan komai .Kumai, kuma babu dabara Babu Karfi sai da Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; kuma ba ma bautawa kowa sai Shi. Ni'ima tasa ce. kuma falala tasa ce. kuma kyakkyawan yabo nasa ne. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. muna masu tsarkake bauta (daga shirka) a gare Shi. ko da kafirai sun ki.

4

(69) Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma godiya ta tabbata ga Allah, kuma Allah Shi ne Mafi girma. (sau talatin da uku) Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki nasa ne (Shi kadai), kuma yabo nasa ne (Shi kadai). kuma Shi ne Mai iko a kan komai.

5

(70) Ina karanta wzd annan surorin (kowacce daga ciki har zuwa karshenta) bayan kowace sallah; amma bayan sallar Asuba da Magariba ana karanta su sau uku.

6

(71) Bayan kowace salla, a karanta Ayatul-kursiyu. Allah. babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye, Mai tsayuwa da komai, Gyangadi ba ya kama Shi, wala barci. Abin da ya ke cikin sammai da abin da yake cikin kasa nasa ne. Babu mai yin ceto a wurinsa sai da izininsa. Yana sane da abin da yake gabansu (wato al'amarin duniya) da abin da yake bayansu (na al'amarin lahira). Ba sa sanin wani abu daga iliminsa, sai abin da Ya so. Kursiyyunsa (wato gadonsa) ya yalwaci sammai da Kasa, kuma kiyaye su (sammai da Kassai) ba ya yi masa nauyi, Shi ne kuma Madaukaki, Mai girma.

7

(72) Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi Kadai, babu abokin tarayya a gare Shi, Mulki nasa ne (Shi kadai), kuma yabo nasa ne (Shi kadai), yana rayarwa, kuma yana kashewa, kuma Shi ne Mai iko a kan komai. (sau goma bayan sallar Magariba da sallar Asuba)

8

(73) Ya Allah! Ina rokonka ilimi mai amfani, da arziki kyakkyawa (wato na halal), da aiki wanda Za a Karba. (bayan sallama daga sallar Asuba)

Zaker copied