(55) Ya Allah! Ina neman tsari da kai daga azaba kabai, da azabar Jahannama, da fitinar rayuwa da ta mutuwa, da sharrin fitinar Dujal shafaffe.
(56) Ya Allah! Ina neman tsarinka daga azabar kabari, kuma ina neman tsarinka daga fitinar Dujal shafaffe, kuma ina neman tsarinka daga fitinar rayuwa da ta mutuwa. ya Allah! Ina neman tsarinka daga laifi da bashi.
(57) ya Allah! Hakika ni na zlunci kai na, zalunci mai awa, kuma babu mai gafarta zunubai sai kai. Saboda haka ka gafarta mina, gafara daa gare ka, kuma ka ji kai na, lallai kai ne Mai yawan gafara, Mai yawan jin kai.
(58) ya Allah! Ka gafarta mini abin day a wuce da abin da zai zo, da abin da na boye da abin da na bayyana, da kima abin da kai ne ka fi ni daninsa. Kai ne mai gabatarwa, kuma kai ne Mai jinkirtarwa; babu abin bautawa da gaskiya sai kai.
(59) ya Allah! Ka taimake ni a kan zikirinka da yin godiya gare ka du kyautata ibada gare ka.
(60) ya Allah! Ina neman tsarinka daga rowa, kuma ina neman tsarinka daga tsoro, kuma ina neman tsarnka da a maida ne zuwa wulakantcciyar rayuwa (tsufa tukuf-tukuf), kuma ina neman tsarinka daga fitinar duniya da azabar kabari.
(61) ya Allah! Ina rokon ka aljanna, kuma ina neman tsarinka daga wuta.
(62) ya Allah! Saboda Saninka da abin day a faku, da kuma Ikonka a kan halitta, Ka rayar da ni idan ka san rayuwa ta fi alheri a gare ni, kuma ka kasha ni idan ka san mutuwa ta fi aheri agare ni, ya Allah! Ina rokonka jin tsoronka a boye da kuma a sarari, kuma ina rkaonka fadar gaskiya a halin dadin raid a halin fushi, kuma ina rokonka tsakaitawa a cikin wadata da talauci, kuma ina rokonka ni'ima dab a ta karewa, kuma ina rokonka sanyin idaniya (wato fain ciki) dab a ya yankewa. Kuma ina rokonka yarda da kaddara bayan afkuwarta. Kuma ina rokonka rayuwa ta ni'ima bayan mutuwa. Kama ina rokonka dadin kallon fuskarka, da kumaashaukin saduwa da kai, ba tare da cuta cutarwa ba, ko fitina mai bataarwa, ya Allah! Ka yi mana ado da adon imani, kuma ka sanya mu masu shiryarwa kuma shiryayyu.
(63) ya Allah! Ina rokonka, ya allah, saboda kai ne Daya kadai tal. Wanda ake nufa da dukkan bukatu, Wanda bai Haifa ba, kuma ba a haife shi ba, kuma babu wani tamka a gare Shi, ka gafarta mini zunubai na, kai ne Mai yawan gafara. Mai yawan jin-kai.
(64) Ya Allah! Ina rokonka saboda dukkan yabo ya tabbata gare Ka, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, kai kadai, babu abokin tarayya a gare Ka, Mai yawan bajwa; ya Makagin halittar sammai da Kasa. ya Ma'abocin girma da alheri. ya Rayayye. ya Mai tsayuwa da komai, ina rokonka aljanna, kuma ina neman tsarinka daga vmta.
(65) Ya Allah! Ina rokonka, saboda ni na shaida cewa Kai ne Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Kai Kadai tal, Wanda ake nufa da dukkan bukatu, Wanda bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba, kuma babu wani tamka a gare Shi.