Addu'ar Sujada

1

(41) Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mafi daukaka (sau uku) .

2

(42) Tsarki ya tabbata gare ka, ya Allah, ya Ubangijnmu! Tare da gdiya gare ka, Ya Allah! Ka gafarta mini.

3

(43) (Ubangiji) abin tsarkakewa, mai kubuta daga dukkan abin da bai kamace shi ba, Ubangijin Mala'iku da Jibrilu.

4

(44) Ya Allah! Gare ka na yi sujada, kuma da kai na yi imani, kuma gare ka naamafa wuya. Fuskata ta yi sujada ga Wanda ya halicce ta, kuma ya ui mata surarta, kuma ya tsaga ji da gani agare ta. Allah mafi gwanintar masu halitta, ya girma, kuma alherinsa ya yawaita.

5

(45) Tsarki ya tabbata ga (Allah) Mai dole, da mulki, da kasaitar daukaka da girma.

6

(46) Ya Allah! Ka gafarta mini zunubaina dukkaninsu, kananansu da manyansu, na farkonsu da na karshensu,bayanannunsu da boyayyunsu.

7

(47) Ya Allah! Ina neman tsari da Yardarka daga Fushinka, da kuma Rangwmnka daga Ukubarka, kuma ina neman tsari da kai daga gare ka ban isa na tuke ga yabo mai cancanta gare ka ba; kai dai kamar yadda ka yabi kanka ne.

Zaker copied