Addu'ar dagowa daga Ruku'u

1

(38) Allah ya ji wanda ya gode masa.

2

(39) Ya Ubagijinmu! Dukkan yabo ya tabbata gare ka, yabo mai yawa, kyakkyawa, kuma abin saw a albarka a cikinsa .

3

(40) Ya Ubangijinmu! Dukkan yabo ya tabbata gare ka, (yabo) mai cika sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu, mai cika duk abu da ka so bayan haka. Ya wanda ya cancanci yabo da daukaka, (Wannan yabo) shi ne mafi cancantar abin da bawa ya fada, kuma dukkaninmu bayi ne gare ka, Ya Allah!Babu mai hana abin da ka bayar, kuma babu mai bayar da abin da ka hana, kuma wadata bat a tsirar da mai wadata daga gare ka.

Zaker copied