Addu'ar Ruku'u

1

(33) Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma.

2

(34) Tsarki ya tabbata gare ka, ya Allah, ya Ubangijinmu, tare da godiya gare ka. Ya Allah! Ka gafarta mini.

3

(35) (Ubangiji) abin tsarkakewa, mai kubuta daga dukkan abin da bai kamace shi ba, Ubangijin mala'iku da Jibrilu.

4

(36) Ya Allah! Gare ka na yi ruku'u, kuma da kai na yi imani, kuma gare ka na mika wuya, Jina ya yi kaskanci gare ka, haka ma ganina da bargona, da kashina, da jijiyata, da kuma abin da kafata ke dauke da shi.

5

(37) Tsarki ya tabbata ga (Allah) Mai dole, da mulki, da kasaitar daukaka, da girma.

Zaker copied