Addu'ar bude sallah (wato bayan an yi kabbarar harama)

1

(31) Ina girmama Allah girmamawa, Ina ginnama Allah girmamawa, Ina g mawa, kuma yabo ya tabbata ga Allah, mai yawa, yabo ya tabbata ga Allah, mai yawa, yabo ya tabbata ga Allah, mai yawa, Tsarki ya tabbata ga Allah a safiya da yammaci (sau uku). Ina neman tsari da Allah daga Shaidan, daga hurawarsa, da to finsa da kuma zungure-zungurensa.

2

(27) Ya Allah! Ka nisanta tsakanina da laifuffukana kamar yadda ka nisanta tsakanin gabas da yamma: ya Allah! Ka tsakanin ni daga laifuffukana kamar yadda ake tsarkake farar tufa daga dauda; Ya Allah! Ka wanke ni daga laifuffukana da kankara da ruwa da raba.

3

(28) - Tsarki ya tabbata gareka Ya Allah, tare da yabo gareka; Albarkatun Sunanka sun yawaita; Mulkinka da girmanka sun daukaka; babu abin bautawa da gaskiya ba kai ba.

4

(29) Na juya fuskata ga wanda ya kagi halittar sammai da kassai, ina mai karkata ga addini na gaskiya, kuma nib a na cikin mushrkai lallai sallata da ayyukan ibadata da rayuwata da mutuwata na Allah ne. Ubangijin talikai; babu abokin tarayya a gare Shi.kuma da wannan aka umarce ni, kuma ni ina daga cikin musulmi Ya Allah! Kai ne Sarki, babu abin bautawa da gaskiya sai kai; kai ne ubangijina, kuma ni bawanka ne; ka gafarta mini zunubaina dukkaninsu ba wanda yake gafarta zunubai sai kai; ka shiryar da ni zuwa ga mafi kyawun dabi'u, babu wanda yake shiryarwa ga mafi kyawunsu sai kai; ka gusar da nuyagunsu (dabi'u) daga gare ni. Babu wanda zai gusar da miyagunsu daga gare ni, babu wanda zai gusar da miyagunsu daga gare ni sai kai, Na amsa maka, na sake amsa maka. Da biyayya gare ka bayan biyayya; kuma arziki naka ne, kuma alheri dukkaninsa yana Hannunka, sharri kuma ba a dangana shi gare ka. Ni kuma dacewata tana gare ka, kuma gare Ka nake fakewa, Alherinka ya yawaita, kuma ka daukaka, Ina neman gafararka, kuma ina tuba gare ka.

5

(30) Ya Allah! Ya Ubangijin jibailu da mika'ilu da Israfilu! Mai kagen halittar sammai da kassai, Masanun fake da sarari!Kai ne Kake hukunci tsakanin bayinka cikin abin da suka kasance suna sassabawa a cikinsa (na gaskiya). Ka shirye ni Zuwa ga abin da aka sassaba a cikinsa na gaskiya da Nufinka; hkika Kai ne mai shiryar da wanda ka so (shiriyarsa) zuwa ga tafarki madaidaici.

6

(32) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya tashi cikin dare zai yi sallar dare (tahajjudi) yana cewa: Ya Allah! Dukkan yabo ya tabbata gaare ka. Kai ne Hasken sammai da kassai da wanda ke cikinsu; kuma dukkan yabo ya tabbate gare ka. Kai ne Mai tsayar da sammai da kassai da wanda ke cikinsu da karfin ikonka; kuma dukkan yabo ya tabbata gare ka, kai ne Ubangijin sammai da kassai da wanda ke cikinsu; kuma dukkan yabo ya tabbata gare ka, kai ne da sarautar ssammai da kassai da wanda ke cikinsu; kuma dukkan yabo ya tabbata gare ka, kai ne Sarkin sammai da kassai, kuma dukkan ya tabbata gare ka, kai ne gashiya, kuma alkawarinka shi ne gaskiya, kuma maganarka ita ce gaskiya, kuma saduwa da kai it ace gaskiya, kuma aljanna gaskiya ce, wuta ma gskiya ce, Annabawa ma gaskiya ne, (Annabi) Muhammadu ma, tsira da maincin Allah su tabbata a gare shi, gaskiya ne, sa'ar kiyama ma gaskiya ce, Y Allah! Gare ka kadai na maka waya, kuma da kai kadai na dogara, kuma da kai kadai na yi imani, kuma xuwa gare ka kadai nake komawa, kuma saboda kai ne kadai na yi jayayya, kuma gare ka kadai na kai hukunci Don haka ka gafarta mini abin day a wuce da abin da zai zo, da abin da na boye da abin da na bayyana. Kai ne Mai gabatarwa, kuma kai ne Mai jinkirtarwa; babu abin bautawa da gaskiya sai kai, kai ne wanda nake bautawa; babu abin bautawada gaskiya sai kai.

Zaker copied