Daga cikin ayyukan alheri da kyawawan halaye

1

(267) Jabir bin Abdullah, Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. ya Ce: ldan duhun dare ya gabato – ko kuma almuru ta yi - to ku hana ya yanku fita, domin Shaidanu suna bazuwa a wannan lokacin. ldan sa’a ta gota a cikin dare, to sai ku bar su. Ku rufe kofofi, kuma ku ambaci Sunan Allah (yayin da kuke rufewa), domin Shaidan ba ya bude kofa rufaffiya. Ku zuge bakin salkunan ruwanku, kuma ku ambaci Sunan Allah (yayin da kuke zugewa), kuma ku rufe kwanukan abincinku, ku ambaci Sunan Allah (yayin da kuke rufewa); ko da ku dora wani abu ne a kan kwanukan. Kuma ku kasha fitilunku na a-ci-balbal. Allah ya yi tsira da aminci da albarka ga Annabinmu Muhammadu. da alayensa, da sahabbansa baki daya.

Zaker copied