Falalar tasbihi, da godiya ga Allah, da yin la ilaha illal lah, da yin kabbara

1

(254) Abu Huraira, Allah ya yarda da shi. ya ruwaito cewa: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tnbbata a gare shi. ya ce. Wanda ya ce. Tsarki ya tabbata ga Allah. tare da godiya gare Shi. (sau dari) a rana, za akankare masa zunubansa ka da sun kasance kamar kumfar teku ne wajen yawa).

2

(255) Abu Ayyub Al-Ansari, Allah ya yarda da shi, ya ruwaito daga Manzon .Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, cewa ya ce: Wanda ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai; babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki ya tabbata gare Shi. kuma yabo ya tabbata gare Shi; kuma Shi Mai iko ne a kan komai. (sau goma) to kamar wanda ya yanta bayi hudu ne daga cikin ya'yan (Annabi) isma'ila.

3

(256) Abu Huraira. Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin .Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Akwai wasu kalmomi biyu masu sauk in fada a harshe, masu nauyi akan mizani (na ayyuka ranar kiyama), masu soyuwa ga (Allah) Mai yawan jin kai (su ne): Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da godiya gare Shi; tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma.

4

(257) Abu Huraira, Allah ya yarda da shi, ya Ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya Ce: Fadin: Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah. kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. kuma Allah ne Mafi girma. .. shi ya fi soyuwa gare ni daga dukkan abin da rana ta hudo a kansa.

5

(258) Daga sa’ad bin Abi Wakkas, Allah ya yarda da shi ya ce: mun kasance a wajen Manzon Allah, tsira da amincin .Allah su tabbata a gare ahi. sai ya ce: yanzu dayanku yana kasa aikata kyawawan ayyuka dubu a kowace rana? Sai wani mutum cikin wadanda suke zaune tare da shi ya cc: Ta yaya dayanmu zai aikata kyawawan ayyuka dubu? Sai ya ce: Ya yi tasbihi (ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah) Sau dari, sai a rubuta masa kyawawan ayyuka dubu ko a kankare masa: zunubai dubu.

6

(259) Jabir Allah ya yarda da Shi. ya ce: Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya Ce; wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma. tare da godiya gare Shi. Za a dasa masa biishiyar dabino Cikin aljanna.

7

(260) Daga Abo Musa Sl-Ash'ari, Allah ya yarda da shi. ya cc: Manzon. Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, ya ce mini: Ya Abdallah bin kais Ba na shiryar da kai ba zuwa ga wata taska daga cikin taskokin aljanna ba? Sai na ce: shiryar da ni Sai ya ce: Ka Ce: Babu dabara babu Karfi sai da Allah.

8

(261) Daga Samura bin Jundub, Allah ya yarda da shi, ya Ce. Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya Ce: Mafi soyuwar zance a wajen Allah shi ne: Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah ne Mafi girma. babu komai a gare ka ko da wane daya daga cikinsu kafara.

9

(262) Sa’ad bin Abi Wakkas, Allah ya yarda da shi, ya Ce: Wani balaraben kauye ya zo wajen Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya ce: koya mini wadansu kalmomi da zan rika fada. Sai ya ce: Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; babu abokin tarayya a gare Shi. Allah ne Mafi girma, (ina girmama Shi) girmamawa. Kuma godiya ta tabbata ga Allah da yawa. Tsarki ya tabbata ga Allah. Ubangijin talikai. Babu dabara babu karfi sai da Allah. Mabuwayi Mai hikima. ..Sai mutumin ya Ce: wadannan na Ubangijina ne. ni kuma nawa fa? Sai ya Ce: Ka ce: Ya Allah! Ka yi mini gafara. Ka ji kai na. Ka shirye ni. Ka azurta ni.

10

(263) Tarik ibn Ashyam Al-Ashja'i. Allah ya yarda da shi, ya Ce: Idan mutum ya musulunta, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya koya masa salla, sannan ya umarce shi ya rifa addu'a da wadannan kalmomin: Ya Allah! Ka yi mini gafara,Ka ji kai na, Ka shirye ni, Ka amintar da ni daga bala‘i. Ka azurta ni.

11

(264) Jabir ibn Abdullah. Allah ya yarda da shi. ya Ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya Ce. Mafificiyar addu'a ita Ce (fadin): Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. kuma mafificin zikiri shi ne (fadin): Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.

12

(265) Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Ayyuka nagargaru masu wanzuwa Sune (fadin): Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. kuma Allah ne Mafi girma. kuma babu dabara babu karfi sai da Allah.

Zaker copied