Istigfari (neman gafara) da tuba zuwa ga Allah

1

(248) Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Na rantse da Allah Ina neman gafarar Allah, kuma ma tuba zuwa gare shi, a kowace rana sama da sau Saba in.

2

(249) Kuma ya Ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Allah. Domin ni ina tuba akowace rana zuwa gare shi sau dari.

3

(250) Kama ya ce. tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: Wanda ya ce: Ina neman gafarar Allah, Wanda babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye, Mai tsayuwa da komai. kuma ina tuba zuwa gare Shi. Allah zai gafarta masa zunubansa ko da zunubin gudu daga fagen fama ne.

4

(251) Kuma ya Ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: Mafi kusancin da Allah yake kasancewa da bawansa a tsakiyar karshen dare he. Don haka idan kana da ikon kasancewa cikin masu ambaton Allah a wannan lokacin, to ka kasance.

5

(252) Kuma ya ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: Mafi kusancin da bawa yake kasancewa da Ubangijinsa yayin da yake sujada ne, don haka ku yawaita addu’a (a cikin sujada).

6

(253) Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: lallai a kan lullube zuciyata kuma ni ina neman gafarar Allah sau dari arana.

Zaker copied