Abin da Wanda ya ji wani ciwo a jikinsa zai ce

1

(243) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Ka sanya hannunka a wajen da yake maka ciwo a jikinka, ka ce: Da sunan Allah (nake neman waraka). (sau uku) Sannan ka ce: Ina neman tsari da Allah da kuma Ikonsa daga sharrin abin da nake ji (na ciwo) kuma nake jin tsoronsa. (sau bakwai)

Zaker copied