Yin Kabbara tare da kowace tsakuwa yayin jifan Jamra

1

(239) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. ya kasance yana yin kabbara tare da kowace tsakuwa idan ya jefi Jamrori uku. Sannan sai ya yi gaba kadan ya yi addu'a yana mai fuskantar alkibla, ya daga hannayensa biyu ya yi addu'ar. Yana yin haka ne bayan jifan jamra ta farko da ta biyu. Amma bayan Jamratul Akaba (Jamra ta karshe). sai ya yi Jafan kawai, ya yi kabbara tare da kowace tsakuwa, sannan ya tafi; ba ya tsayawa ya yi addu’a a wajenta.

Zaker copied