(19) Ya Allah ka sanya haske a cikin zuciyata. Da haske a kan harshena. Da haske a jina. Da haske a ganina da haske a birbishina, da haske a karkashina. da haske a damana, da haske a haguna. Da haske a gabana, da haske a bayana; ka sanya haske a cikin raina, ka girmana haske gare ni, ka girmama min haske, ka sanya haske gfare ni, ka sanya ni (na zama) haske, ka sanya haske a cikin jijiyoyina, da haske a cikin namana. Da haske a cikin jinina. Da haske a cikin gashina. Da haske a cikin fatata. Ya Allah ka sanya mini haske a cikin kabarina, ka kara minu haske. Ka kara mini haske. Ka ba ni haske akan haske.