Addu’ar tsayuwa a kan dutsen Safa da na Marwa

1

(236) Jabir, Allah ya yarda da shi, ya ce, yayin da yake sifanta hajjin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: yayin da ya kusanto Dutsen Safa sai ya karanta: Hakika Dutsen Safa da na Marwa suna daga cikin alamomin da Allah Ya sanya (na addininsa)”. Ina farawa da abin da Allah Ya fara da shi. Sannan ya fara da Dutsen Safa, ya hau shi har sai ya hango Dakin Allah, sai ya fuskanci alkibla, ya kadaita Allah, (ya yi hailala), ya girmama shi (ya yi kabbara) ya ce: Allah ne Mafi girma. Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma, Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Shi kadai; babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki ya tabbata gare Shi. kuma yabo ya tabbata gare Shi: kuma Shi Mai iko ne akan komai. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Shi Kadai. Allah Ya gaskata alkawarinsa. Ya taimaki bawansa. Ya ruguza rundunonin kafirai Shi kadai. Ya karanta wannan zikiri sau uku, yana yin Addu'a bayan kowace marra. Da ya hau Dutsen Marwa ma ya yi kamar yadda ya yi a kan Dutsen Safa.

Zaker copied