Yada sallama a cikin al’umma

1

(224) Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Ba za ku shiga aljanna ba Sai kum yi imani, kuma ba za ku yi imani ba sai kun so juna. Shin ba na nuna muku wani abu da in kun yi shi za ku so juna bu? Ku yada sallama tsakaninku.

2

(225) Ammar, Allah ya yarda da shi, ya ce: Abubuwa uku, wanda duk ya hafa su. ya hada imani: mutum ya yi adalci ga kansa, da ya da gaisuwar sallama a cikin al’umma, da yin kyauta a cikin rashim wadata.

3

(226) Daga Abdullah ibn Umar, Allah ya yarda da shi, ya ce: Wani mutum ya tambayi Annabi, tsira da amincin Allah su Tabbata a gare Shi: wane abu ne a cikin musulunci ya fi alheri? Sai ya ce: Ka ciyar da abinci, kuma ka yi sallama ga wanda kn Sani da wanda ba ka Sani ba.

Zaker copied