(219) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: wanda ya yi salati daya a gare ni, Allah zai yi salati goma a gare shi.
(220) Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: ka da ku mai da kabarina idi; ku yi salati agare ni ko ina kuke, domin salatinku yana isa zuwa gare ni ko a ina kuka kasance’.
(221) kuma Annabi, tsira da amincin. Allah su tabbata a gare shi ya ce: [Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa amma bai yi mini Salati ba.
(222) Kuma Annabi, tsira da amincin Allah Su tabbata a gare shi. Ya ce: Allah yana da wadansu malu'iku matafiya abayan kasa, suna isar mini da sallama daga al'ummata.
(223) Kuma Annabi, tsira da amincin Allah Su tabbata a gare shi ya ce: Babu wani wanda zai yi mini sallama face Allah ya dawo mini da raina na amsa masa sallamarsa.