Addu’ar da mutum zai fada idan wani al’amari ya zo masa na farin ciki ko na bakin ciki

1

(218) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi, ya kasance idan wani al'amari ya zo masa da yake faranta masa rai sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah Wanda saboda Ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika. idon kuma wani al’amari ya zo masa wanda yake ki sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah a cikin kowane hali.

Zaker copied