Addu’ar komowa daga tafiya

1

(217) Abdullahi ibn Umar, Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah, tsira dn amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya kama hanyar dawowa daga tafiya wani yafi, ko aikin hajji ko umra, idan ya hau tudu sai ya yi kabbara sau uku, sannan ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai; babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki nasa ne (Shi kadai), kuma yabo ma nasa ne (Shi kadai); kuma Shi Mai iko ne akan komai. Mu masu komowa ne. masu tuba, masu bauta. kuma masu godiya ne ga Ubangijinmu. Allah Ya gaskata alkawarinsa, Ya taimaki bawansa, Ya ruguza rundunonin kafirai Shi kadai.

Zaker copied