(214) Jabir, Allah ya yarda da shi, ya ce: Mun kasance idan muka hau tudu (a halin tafiye- tafiyenmu) sai mu yi kabbara, (wato mu ce: Allah ne Mafi girma). idan kuma muka zo gangara sai mu yi tasbihi (wato mu ce: Tsarki ya tabbata ga Allah).