Addu'o'in tashi daga barci

1

(1) Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda ya rayar da mu bayan ya dauki rayukanmu, kuma zuwa gare shi tashi yake.

2

(2) Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ba ni lafiya a jikina, kuma ya dawo mini da raina, kuma ya ba ni iznin ambatonsa.

3

(3) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: wanda ya farka da daddare ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , shi kadai, babu abokin tarayya a gare shi; mulki da yabo nasa ne, Kuma shi Mai iko ne bias komai Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Kuma Allah shi ne mafi girma, kaum babu dabara babu karfi said a Allah, Madaukaki, Mai girma. Ya Ubangijina! Ka gafarta mini . Wanda ya fad i wannan za a gafarta masa, idan kuma ya yi addu'a za a amsa masa, ikan kuma ya tashi ya yi alwala, ya yi sallah za a kar bi sallarsa

4

(4) Hakika a cikin halittar sammai da kassai, da sabawar dare da rana, lallai akwai ayoui ga ma'abuta hankula. (Su ne) wadanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma a zaune da kuma a kishingide, suke kuma tunani a kan halittar sammai da kassai (sunna cewa): Ya Ubangijinmu!Ba ka halicci wannan abu a banza ba. Tsarki ya tabbata gare ka, ka kiyashe mu azabar wuta, ya Ubangijinmu!Hakika Kai, Kuk wanda Ka shigar das hi wuta, babu shakka ka kunyata. Shi. Azzalumai kuwa bas u da wasu mataimaka. Ya Ubangijinmu Hakika mu. Mun ji mai kira yana kira zuwa ga imani. Cewa: ku yi imani da Ubangijinku. Sai muka yi imani to, ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu, ka kuma kankare mana miyagun ayyukanmu, ka kuma karbi rayukanmu tare da mutane na gari. Ya Ubangijinmu! Ka ba mu abin da ka yi mana alkawari das hi a kan harshen manzannunka, kada kuma ka kunyata mu ranar alkiyama. Hakika Kai ba ka saba alkawari. Shi Ubangjiinsu ya amsa musu (cewe): Hakika, Ni b zan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikinku, namiji ko mace; sashinku daga sashi yake. To, wadanda suka yi hijira, aka kuma fitar das u daga gidajensu, aka cuce su saboda Ni, suka kuma yi yaki, kuma aka kasha su, lallai zan kankare musu miyagun ayyukansu, kuma lallai zan shigar das u aljannatai wadanda koramu suke gudana ta karkashinsu; (wannan) sakamako ne daga Allah. Allah kuwa a wurinsa kyakkyawan sakamako yake. Kada kai-koman wadanda suka kafirta a cikin garuruwa ta rude ka. Jin dadi ne dan kankani; sannan sakamakonsu wutar jahannama ce, tir da wannan makwanta. Amma wadanda suka ji tsoron Ubangijinsu, suna da aljannatai wadanda foramu suke gudana ta karkashinsu, masu dawwama a cikinsu; wannan liyafa ce daga wajen Allah; abin da kuwa ya zo daga wajen Allah shi ya fig a managarta. Kuma hakika akwai daga ma'abuta Littafi wanda yake yin imani da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ku, da abin da aka saukar zuwa gare su, suna masu Kankan da kai ga Allah, bas a musanya ayoyin Allah dad an tamani kankani, Wdancan suna da ladansu a wurin Ubangijinsu, Hakika Allah Mai hanzarta hisabi ne yak u wadanda suka yi imani! Ku yi hakuri, kuma ku rinjayi kafirai acikin hakuri, kuma ku yi zaman dako, kuma ku ji tsoron Allah ko kwa rabauta. [ali Imran. 190 zuwa karshen surar].

Zaker copied